An shawarci manoman Doya, su rungumi sabuwar dabarar shuka ganyen da aka yi wa aure, musamman don kara bunkasa nomanta da kuma samun kudaden shiga masu yawa.
Shugaba a sashen hukumar gudanar da binciken aikin noma (IITA), Dakta Baetrice Aighewi ce ta bayar da wannan shawara a jawabinta na taron kwana guda a Abuja, na dabbaka dabarar shuka ganyen Doyar da ake yi wa aure da kuma amfani da kimiyyar zamani wajen noma Irin Doyar.
- Mutum 10 Sun Mutu A Turmutsutsin Rabon Shinkafa A Abuja
- Kamfanin NNPCL Ya Rage Farashin Litar Mai Zuwa Naira 965 A Abuja
Dakta Baetrice ta bayyana cewa, rungumar wannan sabuwar fasaha, za ta kasance wata babbar dama ga daukacin manoman Doyar da ke fadin kasar nan.
An dai samar da wannan sabuwar kimiyyar zamani ce, karkashin shirin tsarin samar da Irin noma na fasaha (PROSSIVA), wacce kuma aka yi amfani da ita wajen kara bunkasa samar da Irin noma na Doya.
Dakta Baetrice ta kara da cewa, wannan sabuwar fasaha; za ta kara wa masu sarrafa Irin noma kwarin guiwa, idan suka rungumi kimiyyar zamani, wanda hakan zai kuma kara havaka kasuwancinsu tare da kara bunkasa kasuwansu.
Ta ci gaba da cewa, “Manufar shirin shi ne; don samar da ingantaccen Irin Doya daban-daban, musamman ga manoman na Doya.”
Dakta Baetrice ya bayyana cewa, bisa samar da wannan sabuwar kimiyyar ta zamani, manoman Doya za su iya samun daga tan 30 zuwa 50 na Doyar a kowace hekta daya a gonar da shuka Irin Doyar, savanin samun tan 10 da manoman ke samu a gonakinsu.
Shi kuwa, wani kwararre da ke aiki kan wannan kimiyya ta zamani; Dakta Daniel Aihebhoria, zagayawa ya yi da manoman cikin gonakin demo; domin nuna musu a zahari irin alfanun amfani da wannan kimiyya, inda zagayawar ta zo daidai da lokacin girbin gonakin da ake yin girbin Doyar da aka yi amfani da kimiyyar.
Daniel ya sanar da cewa, sakamakon da aka samu ta hanyar amfani da wannan kimiyya; ko shakka babu abin kawatarwa ne.