Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya. A yau shafin namu zai yi magana ne akan amfanin Alo Vera a jikin mace.
Alo Bera tana daya daga cikin abubuwan da ake amfani da ita wajen gyara jiki, tana gyara jiki sosai Aloe Vera tana gyara fuska, tana cire tabon fuska da duk wani tabo na kwarajen fuska har ma da wannan baki-bakin saman ido da kasan ido.
- Nijeriya Ta Koma Ta 44 A Fagen Kwallon Kafa A Duniya
- Gabatowar Kidaya: Jan Hankali Ga Jama’ar Kano
Ga Yadda Uwargida za ki yi amfani da ita:
Idan kika samu Alo Vera sai ki wanke ta sannan ki samu wuka ki raba ta biyu a tsaye, wannan ruwan nata mai yauki nan na ciki shi za ki sa wuka ki kwashe shi sai ki shafa a fuskarki ko kuma idan duk jikinki za ki yi za ki iya nika shi, sannan sai ki shafa ki bar shi ya yi kamar awa daya kafin ki wanke za ki ga yadda fatar jikinki za ta yi. Idan kina amfani da Alo Vera za ta yi laushi ta yi santsi ta yi sheki da kyalli.
Uwargida Alo Vera tana da matukar kyau ga mace tana sauri jika mace tana saurin saukarwa mace ni’ima.
Idan kika samu Aloe Vera sai ki wanke ta sannan ki raba ta biyu a tsaye wannan de ruwan nata mai yauki shi ne za ki diba, bayan kin yi tsarki na karshe kafin ki kwanta sai ki sa wannan ruwan mai yaukin na Alo Bera da kika diba a gabanki wato ki yi matsi da shi. Gaskiya uwargida yana da kyau sosai fiye da yadda bakya zato, kar ki yanka Aloe Vera kafin lokacin da za ki yi shi, an fi so kina yankawa ki sa kar ki barta ta sha iska.
Sannan Uwargida Aloe Vera tana kara tsawon gashi da kyau da laushi. Idan kika yanka ta wannan dai ruwan yaukin shi ne za ki cire ki nika shi sai ki shafa a gashin kamar shamfu ki barshi kamar na tsawon awa daya zuwa biyu sai ki wanke.