Kankana na daya daga cikin kayan itatuwa, wadanda ake yi wa lakabi da kayan marmari. Babu shakka, tana da matukar amfani a jikin Dan Adam, sannan kuma komai nata na da amfani; babu abin yarwa. Ga wasu muhimman bayanai daga cikin amfanin shan ta kamar haka:
Kankana na dauke da sindarin ‘Lycopene’, wanda yake bayar da gagarumar gudunmawa kwarai da gaske wajen kawar da kwayoyin cutar daji.
- Mi’ara Koma Baya-Taylor Ya Koma Alkalancin Gasar ‘Yan Dagaji Ta Kasar Ingila
- Mi’ara Koma Baya-Taylor Ya Koma Alkalancin Gasar ‘Yan Dagaji Ta Kasar Ingila
Kazalika, kankana na samar da kariya daga illolin zafin rana da kuma haske.
Masu yawan shan kankana, suna matukar amfanuwa domin kuwa tana inganta lafiyarsu tare da hana su kamuwa da cutar asma ‘asthma’, dalili kuwa tana dauke da sindarin ‘Bitamin C’.
Haka nan, kankana na samar da kariya daga cututtukan da suka shafi zuciya.
Bugu da kari, ‘ya’yan kankana na da mai, sannan wannan mai na taimaka wa kwarai da gaske wajen gina jiki tare da inganta shi.
‘Ya’yan kankana na dauke da sinadarin ‘amino acids’, wannan sinadari na kara wa Dan Adam lafiyar jiki da karfi da kuma kuzari yayin yin jima’i.
Har ila yau, kankana na taimakawa matuka gaya wajen kara kaifin basira da tunanin Dan Adam.
Sa’annan, da zarar matum ya yi rashin lafiya ya samu sauki; yana bukatar samun kankana ya sha, domin kuzarinsa da jininsa ya samu ya dawo jikinsa.
Kankana tana dauke da sindarin da ke bayar da kariya tare da rage cutar hawan jini.
Har wa yau, uwargida za ta iya yin jus din kankana domin inganta lafiyarta tare da kara mata ni’ima da inganci da kuma na maigida, kai har ma da yara baki-daya dukkaninsu za ta gyara su.
Kadan kenan daga cikin amfanin kankana wadda ake yi wa kirari da uwar ruwa. Don haka, uwargida da maigida ka da ku bari a bar ku a baya, domin kankana na da matukar amfani a gare mu baki-daya.
Mun rubuto daga Turakar Dakta Maryam A.A