• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amfanin Man Kade A Gyaran Fatar Jikin Mace

by Amina Bello Hamza
3 years ago
Mace

Kadanya wata bishiya ce da ta ke samar da ‘ya’ya koraye ma su zaki. Kwarai kuwa ‘ya’yan kadanya korra ne ko da sun nuna. Daga ‘ya’yan ne ake samar da man kadanya bayan an sarrafa su.

Wasu mutanen na kiran sa man kade, yayin da wasu ke kiran sa da man kadanya. Ko da wanne suna ka san shi, ba shakka man kadanya  na da matukar amfani wajen inganta lafiyar dan-adam.

  • A Sake Lale Kan Mayar Da Tubabbun ‘Yan Boko Haram Jihohinsu Na Asali
  • Majalisa Ta Tabbatar Da Arase A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yansanda

Tun zamani mai tsawo da ya shude ake amfani da man kadanya wajen samar da magungunan kan wasu matsalolin lafiya musamman matsalolin da su ka shafi fata saboda man kadanya na kunshe da sinadarai da dama da su ka hada da sanadaran Bitamin A, Bitamin E, Calcium da sauran su.

Daga cikin amfanin man kadanya, akwai maganin kurajen fuska da sanya laushin fata da maganin kyasbi, hakanan ana amfani da man kadanya wajen maganin fason kafa da bushewar fata, da dai sauran amfani da man kadanya ke samar wa dan adam.

Ba tare da bata lokaci ba, za mu kawo wasu daga cikin amfanin man kadanya wajen inganta lafiyarmu.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

  1. Amfanin man kadanya wajen maganin fason kafa; Ana amfani da man kadanya sabuda maganin fason kafa. Don samun wannan amfani na man kadanya, mutum zai yi takidin mansa mai kyau, idan dare ya yi kafin ya kwanta, sai ya goge kafarsa sannan ya shafDat da man kadanya, sai ya sanya kafar cikin leda sannan ya sanya cikin safa, idan gari ya waye sai ya cire ya wanke. Haka zai juri yi musamman idan a lokacin hunturu ne, da sannu zai ga abin mamaki.
  2. Man kadanya na maganin kyasbi; Hakanan ana amfani da man kadanya don maganin kyasbi. Idan mutum zai hada maganin kyasbi da man kadanya, sai ya samu man sandal da man ‘labender’ ya zuba cikin man kadanya sannan ya kwaba sosai sannan ya samu mazubinsa mai kyau kuma mai murfi ya zuba wannan hadin ya adana.

Yadda zai yi amfani da shi, shine, ya mayar da wannan hadin  manmnyka tamkar man shafawasa, ma’ana  zai ke yin amfani da wannan hadin a kullum har tsawon watanni shida. Idan Allah Ya so za a dace.

  1. Ana amfani da man kadanya don laushin fata; Ga wanda ya ke son fatarsa ta kasance mai laushi, shin mace ce ko namiji sai ya yawaita shafa man kadanya a duk ilahirin jikinsa bayan ya/ta yi wanka. Ba shakka yin hakan na sanya laushin fata.
  2. Man kadanya na rigafika wasu cutukan fata; An samu sahihin bayani game da yadda man kadanya ke yin riga-kafin wasu cutukan fata. Idan mutum na yawan amfani da man kadanya zai samu kariya daga kamuwa daga wasu cutukan fata. Idan ya so zai yi amfani da man kadanya kamar yadda mu ka ambata a lamba ta 3 da ke sama.
  3. Man kadanya na maganin gautsin fata; Wasu mutanen Allah Ya jarrabe su da gautsin fata. Da zarar fatarsu ta sha wahala ba wuya ta samu lahani, to ma su fama da irin wannan matsala ta gautsin fata na iya amfani da man kadanya don samun waraka.

Duk mai fama da wannan matsala ya samu man kwakwa da man zaitun da kuma man ‘almond’ ya hada su ukun da man kadanya ya kwaba su, ya tabbatar sun kwabu sosai, sai ya zuba a cikin mazubinsa mai kyau kuma mai murfi ya adana. Wannan hadin zai rika shafawa a dukkan jikinsa. Don samun cikakkiyar fa’ida sai ya mayar da man kadanya matsayin man shafawarsa kowanne lokacin idan ya fito daga wa

  1. Man kadanya na maganin bushewar labe; A samu zuma da man zaitun sannan sai a zuba a kan man kadanya a kwaba sosai. Sannan a sa a wuri mai sanyi . Sai a rika shafawa a labban baki a kullum za a samu sauki.
  2. Ana amfani da man kadanya don gyaran gashi; yawaita Kitso da man kadanya na magance wasu cutukan fatar kai kamar, makero sannan yana sanya gashi laushi da tsayi da kuma sulbi.
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
An Gudanar Da Bikin Baje Koli Na Bikin Bazara Na Kantunan Littattafan Kasar Sin A Ketare Karo Na 13 

An Gudanar Da Bikin Baje Koli Na Bikin Bazara Na Kantunan Littattafan Kasar Sin A Ketare Karo Na 13 

LABARAI MASU NASABA

Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

October 15, 2025
Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari 

Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari 

October 15, 2025
Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji 

Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji 

October 15, 2025
Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano

Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano

October 15, 2025
Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar

Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar

October 15, 2025
Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia

Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia

October 15, 2025
Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya 

Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya 

October 15, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

October 15, 2025
An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou

An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou

October 15, 2025
sallah

Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02%

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.