Kamar yadda masana suka bayyana, namijin goro na da matukar amfani ta fuskoki da dama, musamman a bangaren da ya shafi magunguna, karin kuzari da sauran makamantansu. Ga amfanin da namijin goron ke da shi 16 kamar haka:
– Namijin goro na maganin tari; idan aka hada shi da alawar tomtom aka ci a tare.
– Kazalika, namijin goro na maganin matsalar ciwon sanyi; idan aka hada shi da kanumfari a tafasa a ruwa aka rika sha.
– Namijin goro yana maganin matsalar tsutsar ciki; idan aka jajjaga shi aka matse ruwan, sai a zuba zuma a rika sha.
– Haka nan, namijin goro na maganin olsa, idan aka hada shi da dabino aka daka, sai a zuba zuma cokali biyu a sha.
– Wakazalika, namijin goro na maganin kara kuzari da nisan tafiya ga masu iyali, idan aka hada shi da dabino sai a rika tauna su tare.
– Namijin goro na gyara maniyyi, idan aka jajjaga shi aka samu garin hulba aka tafasa, sai a samu madarar ruwa a zuba a shanye baki-daya.
– Sannan, namijin goro na kawar da majinar kirji, idan ana cin sa lokaci zuwa lokaci.
– Namijin goro na hana shan taba, idan aka hada shi da furen tumfafiya, aka dake aka samu karan sigari da madarar shanu mai kyau, a hada guri guda a bar su su kwana da safe kafin a ci komai, sai mai shan tabar ya shanye duka. Bayan wasu mintuna ko awanni zai yi aman dattin tabar baki-daya, sannan ba zai kara sha’awar sake ba da yardar Allah.
– Har ila yau, namijin goro yana maganin hawan jini, idan aka hada shi da ganyan cediya; sai a tafasa a sa zuma a sha.
– Namijin goro na maganin ciwon kai, idan aka dake shi ya zama gari, sai a rika yin hayaki (turare) da shi, musamman ma mata masu yawan ciwon kai.
– Namijin goro yana gyara murya, idan aka hada shi da danyar citta da zuma, ana dafawa da lifpton a sha kafin a ci komai da safe.
– Namijin goro na maganin kuraje, idan aka samu garin namijin goron; aka kwaba da man zaitun. Idan kuma karzuwa ce ko bakon dauro, sai a kwaba da manja a rika shafawa.
– Haka nan, namijin goro na maganin sanyin mara, idan aka hada da kanunfari da lemon tsami da Citta da garin albabunaj, sai a tafasa a rika sha da zuma.
– Namijin goro na maganin kuna, idan aka hada da sassaken itacen kirya aka daka, sai a rika barbadawa a kan kunar.
– Namijin goro na tsayar da jini, idan aka hada da tsamiya aka tafasa, sai a sha nan take jinin zai tsaya da izinin Allah.
– Bugu da kari, namijin goro yana kawar da wasu cututtuka da suke a cikin mutum iri daba-daban.