Ranar 10 ga watan nan da muke ciki, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu kan umarnin kara buga harajin kwastam na kashi 25% kan ma’adanan karfe da goran ruwa da za a shigo da su cikin kasar. Yana mai bayyana cewa, Amurka za ta aiwatar da wannan mataki kan dukkan kasashe ba tare da ba da kariya ga wasu ba.
Duniya na sabawa da hakan duba da cewa, a cikin wa’adin aikinsa na farko, ya taba buga karin harajin kwastam na kashi 25% kan karfe da na kashi 10% kan goran ruwa. Burin Donald Trump shi ne, gaggauta dawo wa masana’antun samar da kayayyaki cikin gida da tabbatar da samar da guraben aikin yi ga Amurkawa da kara wa gwamnatin Amurka kudin shiga ta amfani da matakin harajin kwastam. Amma, idan an waiwayi tarihi, Amurka ba za ta cimma burinta ba ko kadan.
- Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
- Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota
Babban darektan cibiyar nazarin aikin sa ido da kasuwa na kwalejin Brookings na Amurka Sanjay Patnaik ya yi nazari kwanan baya cewa, harajin kwastam ba zai ba da tabbaci ga samar da guraben aikin yi a sana’o’in karfe ba, duba da cewa, karin harajin kwastam zai haifar da karin kudin da sana’o’in za su kashe, har ma da rage kayayyakin da za a samar, shi ya sa zai haifar da raguwar daukar ma’aikata a wannan bangare.
Ba shakka, ba wanda zai yi nasara a cikin yakin harajin kwastam da na ciniki ko kadan ba, wannan ita ce tsabar gaskiya da aka tabbatar ba daya ba, ba biyu ba.
Dole ne gwamnatin Amurka ta saurari bukatun abokan cinikinta, ta kula da moriyar kamfanoni da masu sayayyarta, ta koma hanyar takara mafi dacewa. Saboda kalubale kawai manufar kariyar cinikayya ke haifarwa a maimakon ba da tsaro. (Amina Xu)