Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da mai ba da taimako ga shugaban Amurka kan harkokin tsaron kasar Jake Sullivan a jiya Alhamis a nan birnin Beijing. Yayin ganawarsu, Xi ya jaddada muhimmancin kwarai ga sanin babban tsari mafi dacewa na raya huldar kasashen biyu, yayin da kasashen biyu ke tuntubar juna, wato da farko, a fahimci shin huldar kasashen biyu ta abokantaka ce ko ta hamayya.
A cikin shekaru baya-bayan nan, sau da dama kasar Sin ta bayyanawa Amurka muhimmancin da take dorawa kan wannan batu. Dalilin da ya sa Sin ta dade tana nacewa kan wannan matsayi shi ne, baiwa bangaren Amurka jagoranci ta yadda zai janye daga ra’ayin wani bangare ya samu riba shi kadai, da fahimtar cewa, Sin na kokarin samun bunkasuwa don amfanar jama’arta, kuma Sin ba ta da nufin maye gurbin Amurka. A sa’i daya kuma, ba wanda zai iya kwace hakkin Sinawa na samun ci gaba.
- Xi: Sin Da Afirka A Ko Da Yaushe Al’umma Ce Mai Makomar Bai Daya
- Sin Ta Bayyana Matsaya Game Da Wasu Muhimman Batutuwa Biyowa Bayan Ziyarar Sullivan A Kasar
An lura da cewa, a ziyararsa a wannan karo, Jake Sullivan ya jaddada matsayin da shugabannin kasashen biyu suka amincewa a yayin taron tsibirin Bali na shekarar 2022, wato Amurka ba za ta nemi canja tsarin mulkin Sin, da ta da sabon yakin cacar baka, da yaki da Sin ta hanyar karfafa kawancenta da wasu sassa ba, kana za ta kauracewa goyon bayan masu yunkurin neman ’yancin kan yankin Taiwan da hana tada rikici da Sin.
Kaza lika ya jaddada burin Amurka na zama tare cikin lumana da Sin. Kari kan haka, abu mafi muhimmanci shi ne Amurka ta tabbatar da wadannan ra’ayoyi a aikace, kada ta nuna fuska biyu.
Huldar Sin da Amurka na da muhimmanci matuka a duniya, alakarsu ta wuce batun cimma muradun kasashen biyu su kadai, domin alakar su na jan ragamar ci gaban duniya, don haka dole ne bangarorin biyu sun fidda wata hanya mafi dacewa duk da sauye-sauyen da ake fuskanta. (Amina Xu)