• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amurka, Kasar Da Ke Kawo Cikas Ga Kokarin Duniya Na Shawo Kan Annobar Covid-19

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

Annobar Covid-19 matsala ce da ke addabar duniya baki daya, wadda ke bukatar hadin gwiwar kasa da kasa don shawo kanta. Sai dai abin takaici shi ne, cikin shekaru uku da suka wuce, kasancewarta babbar kasa mafi karfi a duniya, Amurka ta yi ta kawo cikas ga kokarin kasa da kasa na shawo kan cutar, a maimakon daukar nauyin da ke rataye a wuyanta.

A matsayinta na kasa mai ci gaban aikin kiwon lafiya a duniya, mahukuntan kasar ta Amurka ba su dauki matakan da suka kamata ba na tinkarar annobar, inda suka yi biris da lafiyar al’umma da rayukansu, kuma a maimakon haka, sai suka mai da hankali a kan siyasantar da annobar, matakin da ya sabbaba saurin yaduwar annobar.

  • Shugaba Talon Na Benin Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin

A cikin shekarun uku da suka wuce, an samu yaduwar kusan dukkanin nau’o’in cutar Covid-19 a kasar, inda sama da ’yan kasar miliyan 100 suka harbu da cutar, baya ga kuma sama da miliyan daya da suka rasa rayukansu. Ban da haka, gwamnatin kasar ba ta dauki mataki na kayyade harkokin fita daga kasar ba, inda ta bar cutar ta rika yaduwa zuwa sauran sassan duniya.

Alkaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, daga watan Afrilun shekarar 2020 zuwa watan Maris na shekarar 2021, gaba daya al’ummar kasar miliyan 23 da dubu 195 suka fice daga kasar, wadanda suka tafi sassa daban daban na duniya. Sa’an nan, yadda kasar ta tilastawa bakin haure da su koma kasashensu na asali ba tare da lura da yanayin lafiyarsu ba, ya kara tsananta yanayin annobar da kasashen Latin Amurka ke ciki.

A yayin da duniya ke kokarin shawo kan annobar, kasar Amurka ta kuma fice daga hukumar lafiya, baya ga tara dimbin rigakafin cutar a gida, ba tare da raba su ga sauran kasashe masu bukata ba. Alkaluman da cibiyar kandagarkin cututtuka ta Amurka ta samar sun shaida cewa, daga watan Maris zuwa watan Satumban shekarar 2021, Amurkar ta bata a kalla rigakafi miliyan 15.1. Idan ba a manta ba, Amurka ta tura rigakafin da lokacin aikinsa ya kusan karewa zuwa kasashen Afirka, matakin da ya jawo suka daga kasashen.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

In mun waiwayi tarihi, sau tari mabambantan annoba sun haifar da munanan hasarori ga ’yan Adam, kuma tarihi ya shaida cewa, cuta ba ta san iyaka ko kabila ba. Shekaru ukun da suka wuce da ake yaki da cutar Covid-19 ma sun shaida mana cewa, ’yan Adam makomarsu daya ce, kuma siyasantar da annobar ba zai haifar da komai ba illa lalata hadin gwiwar kasa da kasa wajen dakile cutar, tare da haifar da karin hasarori ga al’ummar duniya. (Mai Zane: Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 4 A Neja, Sun Kwace Makamai

'Yansanda Sun Kashe 'Yan Bindiga 4 A Neja, Sun Kwace Makamai

LABARAI MASU NASABA

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid

October 26, 2025

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Wa Masu Ƙananan Sana’o’i Biliyan 75 Domin Bunƙasa Kasuwancinsu

October 26, 2025
Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

Ɗan Majalisa Ya Ce Ba Zai Sake Takara Ba, Ya Sadaukar Da Ita Ga Matasa

October 26, 2025
Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

October 26, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.