Wani sabon babi na takaddamar cinikayya a duniya na kunno kai biyo bayan sabon matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da Sin ke shigowa da su kasarsa, lamarin da ke ci gaba da rura takun sakar kasuwanci a duniya. Tabbas wannan ba maganar haraji ce kawai ba, gwaji ne na juriya, dabaru da tasiri a duniya. Wannan lamarin ya kara kamari bayan da Sin ta mayar da martani ta hanyar ramuwar gayyar kakaba haraji kan wasu kayayyakin Amurka da ke shigowa kasar.
Wannan lamarin dai ba sabon abu ba ne, kuma ya ginu ne a kan takaddamar kasuwanci da ta dade take ci gaba da tabarbarewa a tsakanin kasashen, inda tuni ake musayar kakaba wa juna haraji da takunkumi tare da yin barazana kan kayayyakin juna tun daga shekarar 2018. Yau 10 ga watan Fabrairu ne ake sa ran harajin da Sin ta kakaba wa kayayyakin Amurka zai fara aiki, ko da yake Trump ya ce zai yi magana da shugaban kasar Sin Xi Jinping, don haka ba mamaki a samu maslaha game da batun.
Daga cikin matakan da Sin ta dauka akwai sanya haraji na kashi 10 cikin dari kan kwal da iskar gas LNG, da kashi 15 cikin dari kan danyen mai na Amurka. Kazalika kasar Sin ta sanya harajin kashi 10 cikin dari kan injunan aikin gona, da manyan motocin dakon kaya, da wasu manyan motoci. Za mu iya cewa wannan mataki ba zai yi mummunan tasiri ga masu amfani da wadannan kayayyaki na cikin gidan Sin ba, saboda cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin ta kara zuba jari a kan injunan aikin gona don inganta samar da kayayyaki, da rage dogaro da shigo da kayayyaki daga kasashen waje, da karfafa samar da abinci. Har ila yau, akwai wasu matakan da ba na haraji ba, daya daga cikinsu shi ne wani bincike na yaki da cin hanci da rashawa kan katafaren kamfanin Google na Amurka.
Kasar Sin a shirye take, duk lokacin da Amurka ta ce mata kule tabbas za ta mayar mata da cas, kuma ya kamata fitowar fasahar kirkirarriyar basira ta DeepSeek daga kasar Sin, wadda takunkumin Amurka na hana samar da kwakwalen kwamfuta na Nvidia (chips) ga kasar Sin ya tursasa, wadda ta zama abin al’ajabi a duniyar fasaha, tare da sauya al’amurran da suka jibinci yin amfani da kirkirarriyar basira, ta zama izina ga Amurka. (Mohammed Yahaya)