Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce zai sanar da karbar harajin kwastam na ramuwar gayya kan kayayyakin kasashe daban daban, a yau Laraba, a matsayin wani sabon mataki karkashin yunkurinsa na ta da “yakin harajin kwastam” a duniya. Matakin da shugaba Trump ke son dauka ya janyo damuwa a duniya. Kamar yadda wani masanin al’amuran duniya dan kasar Kenya mai suna Adhere Cavince ya fada, “Manufar kasar Amurka ta zama shingen hana farfadowar tattalin arzikin duniya, da ci gaban kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka.”
Amurka tana kallon kanta a matsayin mai tafka hasara a cinikayyar duniya, lamarin da ya hana ta damar raya masana’antu a cikin gidanta. Kana ta hanyar karbar karin harajin kwastam kan kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar daga ketare, za ta iya daidaita matsalar da take fuskanta. Sai dai ko gaskiya ne haka batun yake?
- Tinubu Ya Tafi Faransa Ziyarar Aiki Na Mako 2
- Tinubu Ya Kori Mele Kyari, Ya Naɗa Ojulari A Matsayin Shugaban NNPC
Hakika, dangane da batun, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi magana mai ma’ana a kwanan nan, yayin ziyararsa a kasar Rasha. Ministan ya ce, duk wata kasa na iya gamuwa da wasu matsaloli, amma ya kamata a dogara da kai wajen neman mafita, maimakon dora laifi kan sauran kasashe. Amurka na son ganin sauran kasashe suna biyanta kudi, don kawai daidaita matsalolinta na kashin kanta da take fuskanta. Sam ba za ta samu biyan bukata ba. Kana manufarta za ta lalata muhallin raya tattalin arzikin duniya, da girgiza imanin da ake da shi kan kasar.
A ganin Shen Yi, farfesa mai nazarin ilimin al’amuran siyasa na duniya, dake aiki a jami’ar Fudan ta kasar Sin, manufar kasar Amurka ta karbar karin haraji ba za ta haifar da da mai ido ba. A cewarsa, idan kowace kasa ta yi wa kasar Amurka ramuwar gayya, kana ba su canza manufofinsu kan sauran kasashe ba, to, za a iya ganin canzawar yanayin kasuwanci a duniya, amma ba tare da samun “farfadowar kasar Amurka” ba. Za a maye gurbin kasuwannin kasar Amurka da na sauran kasashe da yankuna, lamarin da zai mai da Amurka saniyar ware. Cikin dogon wa’adi, jama’ar kasar Amurka za su tafka mafi yawan hasara, kana mutanen duniya za su fara ganin wani sabon yanayin da kasar Amurka da ba ta iya babakere a duniya.
Kana a nahiyar Afirka ma ana samun ra’ayin da ya yi kama da ra’ayin farfesa Shen. Misali, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, a kwanan baya ya taba bayyana cewa, matakin Amurka na karbar karin harajin kwastam zai karfafa kasashen nahiyar Afirka su gaggauta tsayawa da kafafuwansu. A ganin shugaban, kasashen Afirka suna dogaro kan wata hanyar tsarin ciniki da ta hada su da kasashen Turai, wadda aka kafa tun daga lokacin mulkin mallaka. Sai dai wannan tsari ya haifar da illa ga cinikin nahiyar Afirka, saboda har yanzu ba a samu ciniki sosai tsakanin kasashen dake nahiyar ba. Amma sabon matakin kasar Amurka zai sa nahiyar Afirka kara dogaro da kai, da yin karin ciniki a tsakanin mabambantan kasashe dake nahiyar Afirka.
Sanin kowa ne, ciniki mai inganci na bukatar kasuwa mai ‘yanci, da takarar da ake yi cikin daidaito, gami da manufa mai dorewa. Idan kasar Amurka ta ki samar da wadannan abubuwa, to, babu wani abun da za a yi, in ban da mai da kasar saniyar ware, da kara tabbatar da hadin kai tare da sauran abokan hulda. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp