Yayin da gwamnatin Amurka mai cike ta daukar matakan kakaba harajin fito, wanda manazarta da dama ke kallo a matsayin matsin lamba domin cimma burikan kashin kai, shaidu na zahiri na nuna yadda Amurkan ta fara girbar sakamakon wadannan matakai na muzgunawa abokan cinikayyarta.
A zahiri take cewa Amurka ta mayar da karin harajin fito a matsayin wani makami na yiwa sauran sassan kasa da kasa matsin lamba ko barazana, da kokarin samun tarin kudade daga abokanta da ma wadanda take adawa da su.
- Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza
- Ta Yaya Za a Ba Matasa Damar Raya Kansu?
A cewar masana, ta hanyar yin barazanar kakaba haraji, da karya dokokin cinikayya da kasuwanci, Amurka tana ta kara zama saniyar ware, inda mahukuntanta ke kara kebe kasar daga tafiyar hadin kai da lumana da aka saba da ita, sabanin burin da mahukuntanta suka ce suna son cimmawa na “Mayar Da Amurka Gaban Komai”.
Masana da dama sun sha gargadin cewa, kakaba takunkumai hanya ce ta gurgunta tushen da aka gina bunkasar Amurka a kai, kuma mataki ne na raba gari tsakaninta da sauran sassan duniya ta fuskar cinikayya da diflomasiyyar kasa da kasa. Tabbas, kakaba haraji ba zai sa kasashen duniya su martaba Amurka ba, maimakon haka matakin zai kore kasashen da lamarin ya shafa zuwa kulla alaka da wasu sassa na daban.
A daya bangaren kuma, wadannan matakai na kakaba harajin fito da Amurka ke ta matsa lambar aiwatarwa, zai sanya ta rasa matsayinta na ja gaba a fannin shigo da hajoji daga ketare, kamar dai yadda wata kididdiga da hukumar kididdigar kasar ta nuna, cewa a watan Afirilun da ya gabata kadai, Amurka ta samu raguwar hajoji, da hidimomi daga ketare da kaso 16.3 bisa dari a mizanin shekara zuwa dala biliyan 351.
Bugu da kari, a baya bayan nan ma jaridar Financial Times, ta bayyana yadda a yanzu haka adadin hajojin da ake shigarwa Amurka daga sassan duniya daban daban suka ragu zuwa kaso 13 bisa dari, sabanin kaso kusan 20 bisa dari da kasar ke shigowa da su a tsawon shekaru 20 da suka gabata.
Kamar dai yadda kimar Amurka ke raguwa sakamakon matsin lamba da take yiwa sauran sassan duniya abokan cinikayyarta, haka ma wadannan manufofi na kakaba haraji ke fuskantar turjiya, da kyama har daga abokan kasar makusanta. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp