Ofishin Jakadancin Amurka da ke Nijeriya ya yi kakkausar gargaɗi ga ƴan Nijeriya da suke neman zuwa Amurka kawai da nufin su je su haihu a can, tare da cewa, irin wannan tsarin ya saɓa wa dokokin shige da fice ta Amurka.
dabi’ar, wacce aka fi sani da yawon zuwa domin haihuwa, inda hukumomin Amurka suka bayyana da cewa hakan na ɓata tsarin ba da izinin shiga ƙasar wato biza.
A sanarwar da ofishin jakadancin ya wallafa a shafinsa na Tiwita a ranar Litinin, ya ce, an umarci jami’an da ke kula da aikin bayar da iznin zuwa Amurka da su hana dukkanin matan da suke zargin tana nemi buƙatar zuwa Amurka domin kawai ta haihu, domin samar da shaidar zaman Amurka ga ƴaƴansu da suke shirin haifa.
- Amurka Ta Rage Wa’adin Bizar ‘Yan Nijeriya Zuwa Wata Uku
- Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin
“Yin amfani da bizarki wajen yin tafiya kawai domin ki haihu a Amurka don jaririnki ya samu shaidar kasancewa dan Amurka ba a amince da shi ba.
“Jami’an ofishin jakadanci za su hana takardar izinin shigar ku idan su na da dalilin yin imani da wannan shi ne manufarku,” a cewar sanarwar.
Gargaɗin ya yi daidai da irin wannan sanarwar da ofisoshin jakadancin Amurka a Jamaica da Uganda suka fitar kwanan nan, a wani ɓangare na yaƙi da dabi’ar karya ƙa’ida shige da fice.
A cikin watan Janairun 2025, hukumomin Amurka sun sake jaddada aniyarsu na ƙarfafa ikon kula da iyakoki kan yin amfani da damar zama dan ƙasa ta haihuwa.
A farkon wannan shekara, shugaban ƙasar ɗonald Trump ya sake nanata matsayinsa na cewa yaran da aka haifa a Amurka ga baƙin haure ba su da takardun zama ƴan ƙasa kai tsaye.
A bisa dokar da aka yi wa kwaskwarima na Amurka kan shaidar zama dan ƙasa, ta fayyace cewa duk wani jaririn da aka haifa sai an duba matakin damar zaman iyayensa a ƙasar kafin a amince da shaidar zamansa dan ƙasar ko akasin hakan, inda jami’an suka ce ba za a amincewa da wadanda suka shiga ƙasar kawai don an ba su biza ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp