Shirin “Volt Typhoon” dabarar siyasa ce da gwamnatin Amurka ta kitsa, da nufin karkatar da tunanin jama’a, da muzanta wasu kasashe, kamar dai yadda wani rahoto ya nuna.
Cibiyar lura da manhajoji masu cutar da na’ura mai kwakwalwa, da hadin gwiwar hukumar lura da injiniyancin dakunan gwaje gwajen shawo kan manhajoji masu cutar da na’ura mai kwakwalwa na Sin, wadanda suka fitar da rahoton a yau Litinin, sun ce an wallafa rahoton na su ne da nufin fayyace aniyar Amurka, da wasu hukumomin leken asiri, da wasu karin kasashe 5 kawayenta, na kirkirar shirin “Volt Typhoon”, da burin gallazawa kasashen Sin da Jamus da wasu karin kasashe. (Mai fassara: Saminu Alhassan)