Tsohon wakilin kamfanin dillancin labaru na Anadolu na kasar Turkiya a birnin Beijing na kasar Sin Kamil Erdogdu ya rubuta wani sharhi mai taken “Amurka ta lalata manufarta ta fadin albarkacin baki wajen watsa labarai a wannan karo” a kwanakin baya.
Sharhin ya yi nuni da cewa, a ‘yan shekarun baya-bayan nan, kasar Sin ta kara daukar matakai wajen ba da labaran da ke faruwa a kasarta, tare da bude kofarta na maraba da abokai daga ko’ina a duniya don su kawo ziyara kasar. Amma kasar Amurka ta kashe kudade da dama a cikin shekaru 5 da suka wuce don horar da ‘yan jaridan kasashen yammacin duniya da su rika yada jita-jitar dake shafar kasar Sin. Wani masanin Turai Jan Oberg ya bayyana a kwanakin baya cewa, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da wani daftarin doka a shekaru 5 da suka wuce, wanda ya shafi kashe kudi dala biliyan 1.5 don horar da ‘yan jarida da manyan editoci na kasashen yammacin duniya su rika rubuta labarai marasa kyau game da kasar Sin. Manufarsu ita ce yada jita-jita don hana bunkasuwar kasar Sin.
Sharhin ya ce, kasar Amurka ta yi hakan don kawo wa gwamnatinta moriyar tattalin arziki da siyasa. Bayan rushewar tarayyar Soviet, kasar Amurka tana bukatar kirkiro wata sabuwar abokiyar gaba. Bayan da kasar Sin ta kasance kasa ta biyu mafi bunkasuwar tattalin arziki a duniya, kasar Amurka ta mai da kasar Sin a matsayin abokiyar gaba.
Sharhin ya kara da cewa, ‘yan siyasar Washington na kasar Amurka sun kashe kudi fiye da dala biliyan daya don horar da ‘yan jaridan kasashen yammacin duniya yadda za su rika sabawa ka’idojin watsa labarai da yada jita-jita. Wannan batu ya lalata tsarin aikin ‘yan jarida da zubar da kimar jama’ar kasashen yammacin duniya, hakan ba zai zubar da mutuncin Sin a duniya ba, sai ma ya zubar da mutuncin gwamnatin kasar Amurka da na kafofin watsa labarun kasar. (Zainab Zhang)