A yayin taron hukumar daidaita matsaloli ta WTO da aka gudanar a ranar 27 ga watan Febrairu, kasar Amurka ta sake yin amfani da ikonta na hawa kujerar naki don kin amincewa da daftarin zaben sabon alkalin kotun daukaka kara na WTO, wanda membobin hukumar WTO 127 suka gabatar, amma bai samu amincewa a karo na 63 daga bangaren Amurka ba. A madadin wadannan membobin, wakilin kasar Guatemala, ya bayyana cewa, babu wata kafa ta doka da za ta kawo cikas ga tsarin zaben sabbin alkalai, kuma hakan yana tauye hakkin mambobin kungiyar WTO da dama.
Tsarin sulhunta takaddama yana daya daga cikin muhimman ginshikan WTO. Tun bayan da gwamnatin Amurka ta fara kawo cikas ga nadin sabbin alkalai a cikin ‘yan shekarun nan. Kawo watan Disambar 2019, alkali daya ne kadai ya rage a kotun, hakan ya sa kotun ta dakatar da aikinta. WTO ta fuskanci matsala mafi tsanani tun bayan kafuwarta. Kawo ranar 30 ga watan Nuwanban shekarar 2020, dukkan alkalan hukumar sun bar aikin hukumar daukaka kara.
Ka’idojin kasa da kasa ba ka’idojin cikin gida na kasar Amurka ba, bai kamata su samar wa Amurka kadai moriya ba. Wasu mutane a Amurka suna yunkurin yin amfani da karfin Amurka wajen warware takaddamar kasuwanci da kuma tilastawa wasu kasashe yin sassauci, wannan ba wai kawai tauye ka’idojin ciniki cikin ‘yanci ba ne, har ma yana lalata ka’idojin gudanar da harkokin kasuwanci da juna. Bisa tsarin bai daya na raya kasa da kasa da kasancewar manyan bangarori daban daban a duniya, ba zai yiwu Amurka ta gudanar da aikinta bisa ra’ayinta kawai ba. Idan kasar Amurka ta ci gaba da kawo cikas ga ayyukan hukumar WTO, a karshe za ta fahimci laifinta ne, kuma ita kanta wannan matsala za ta shafe ta. (Zainab)