Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris.
Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen duniya suka bai wa matatar.
- Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu
- Alamar Deepseek” Ta Bude Kofar Gyara Na Kara Kunno Kai A Harkokin Duniya
Duba daga rahoton ma’aikatar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta Kpler, ta ce jiragen ruwa shida dauke da kusan ganga miliyan 1.7 na man jiragen sama daga matatar Dangote sun isa tashoshin jiragen ruwa na Amurka a wannan watan na Maris.
Wani jirgin ruwa, Hafnia Andromeda, ana kyautata tsammanin zai isa tashar Everglades a ranar 29 ga Maris tare da kusan ganga 348,000 na man jirgin sama daga matatar Dangote.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp