Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya jaroranci taron manema labarai na yau da kullum Alhamis din nan. Yayin da aka neman amsa daga kasar Sin game da taron WTO da aka gudanar jiya a Geneva, don binciken manufofin cinikayyar Amurka. Sin da EU da Rasha da sauran mambobin kasashe, sun nuna rashin jin dadinsu kan manufofin da Amurka ke dauka wadanda ke sa moriyar Amurka a gaban kome, da keta manufofin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban da gudanar da manufar kare kai da zuga sauran kasashe su yanke hulda da Sin da ma kawo cikas ga tsarin samar da kayayyaki a duniya da sauransu.
Game da wannan batu, Wang Wenbin ya nuna cewa, Amurka ta zama mai zagon kasa ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, mai kawo cikas ga masana’antu da tsarin samar da kayayyaki a duniya, wadda ta kware wajen yin babakere. (Amina Xu)