“Mota a yauzu kasancewar tamkar wayar salula dake da waya, miliyoyin motocin kirar Sin suna tafiya a titunan Amurka, suna tattara bayanan Amurkawa ko da yaushe, sun aike su zuwa Beijing…”, ministar kasuwancin Amurka Gina Raimondo ta yi wannan kalamai maras tushe, abin mamaki ne.
A matsayin wata babbar jami’ar Amurka, kasa mafi karfi a duniya a bangaren ciniki, Gina Raimondo ta ba da jawabi mai ban tsoro maras gaskiya da zummar zuga al’umamr Amurka da su nuna kiyayya ga motoci masu aiki da batura da Sin ta kera, ainihin dalilai sun hadda da na tattalin arziki da ma na siyasa.
Amurka tana sahun gaba a duniya a karni na 20 a bangaren kera motoci, amma ta kasa samun ci gaba a karni na 21. A shekarun baya, Sin tana kara karfin nazarin motoci mai amfani da sabon makamashi, har ta kafa tsarin samar da irin wadannan motoci a duniya. Fadar White House ta fitar da jerin manufofin hana bunkasuwar Sin a fannin kera motoci, Gina Raimondo ta karawa batun kishiri cewa, wai sha’anin da Sin ke gudana kasancewar wata barazana ce, matakin ya biya bukatun kamfanoni da ma’aikatan kera motoci a Amurka, don samun karin kuri’u daga wajensu.
Idan mu yi waiwayi, Amurka ta samu karfi bisa ciniki cikin ’yanci da takarar kasuwanni, amma yauzu ’yan siyasar Amurka suna matukar son yin takara ba bisa adalci ba, amma suna shafawa sauran bakin fenti kawai. “Tsaron kasa” wata hujja ce da su kan amfani da ita, don sanyawa sauran kasashe takunkumi ta yadda za ta hana bunkasuwarsu don kiyaye muradunsu, ba shakka, wannan ya kasance tunanin babakere.
Hana bunkasuwar wani, ba zai karfafa Amurka ba. Dole ne madam Gina Raimondo ta daina fitar da kalamai maras gaskiya, ta dauki matakan da suka dace don ingzia karfin takarar sha’anin kera motocin kasarta. (Amina Xu)