Da yammacin yau Litinin ne jami’ai masu ruwa da tsaki daga ma’aikatar kudi ta kasar Sin, suka yi karin gaske ga manema labarai, game da ziyarar aiki da sakatariyar baitil-malin Amurka Janet Yellen ta gudanar a kasar Sin.
Jami’an sun ce Yellen ta gudanar da ziyarar aikinta tsakanin ranaikun 4 zuwa 9 ga watan nan na Afirilu, inda yayin ziyarar ta gana da firaministan kasar Sin Li Qiang, da mataimakin firaminista He Lifeng, da ma wasu karin jami’ai.
- Hisba Ta Cafke Mata 7 Da Ake Zargi Da Satar Yadidduka A Kano
- Roxy Danckwerts: Ina Matukar Son Rungumar Pandar Kasar Sin
Yayin tattaunawar jami’an, sassan Sin da na Amurka sun amince su hada karfi da karfe, wajen aiwatar da muhimman kudurori da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da ci gaba da karfafa tattaunawa da hadin gwiwa a fannonin raya tattalin arziki da hada hadar kudade, kana su amince da aniyar samar da yanayi mai kyau na gudanar da cinikayya tsakanin kasashen biyu, da harkokin zuba jari tsakanin kamfanonin kasashen, da bunkasa alakar tattalin arziki mai tsafta, da daidaito tsakanin kasashen biyu.
Har ila yau, sassan biyu sun gamsu cewa, ko wace kasa tana da bukatar kare tsaron kan ta. To sai dai kuma Sin ta jaddada cewa, bai dace a dauki batun “Tsaron kasa” wani batu da ya game ko wane bangare ba. Sin ta bayyana damuwa game da yadda bangaren Amurka ke daukar matakai daban daban, irin su kakaba takunkuman dakile kamfanonin Sin, da dorawa Sin karin haraji, da wasu shingayen zuba jari, wanda hakan matakai ne na illata halastattun hakkoki, da moriyar kamfanoni da jama’ar kasar Sin, kana hakan bai dace da moriyar kamfanonin Amurka da jama’ar kasar ba.
A daya bangaren, Sin ta yi maraba da sanarwar da Amurka ta fitar, wadda ke cewa Amurka ba ta da niyyar raba-gari da Sin, kana Sin din na fatan Amurka za ta aiwatar da hakikanin matakai na dakatar da takunkumai, da shingayen da take sanyawa kamfanonin kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)