Taron kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi karo na 29 ko COP29 a takaice, wanda aka kammala ranar Lahadi a birnin Baku na kasar Azarbaijan, ya haska irin babban rashin adalci dake tattare da ayyukan magance sauyin yanayi a duniya. Yayin da al’ummomi a kasashe masu tasowa ke ci gaba da fuskantar kalubale na magance matsalar sauyin yanayi, kokarinsu na ci gaba da fuskantar matsin lamba sakamakon rashin isassun tallafin kudi da tsari daga kasashe masu ci gaba. Wannan rashin daidaito ba wai kawai yana kawo cikas ga yaki na gama-gari da sauyin yanayi ba, har ma yana bayyana ma’auni biyu mai cike da damuwa game da yadda kasashe masu ci gaba ke cin gajiyar albarkatu yayin da kasashe masu tasowa ke fama da matsalolin da sarrafa wadannan albarkatu ke haifarwa.
Duk da kasancewar kasashe masu tasowa ke fitar da mafi karancin hayaki mai gurbata muhalli a tarihi, suna daukar matakai na ban mamaki game da kirkire-kirkire kan magance sauyin yanayi. Kasashe irin su Kenya, Brazil da Grenada sun yi fice a COP29 game da kyawawan ayyukansu da ke da nufin rage mummunar tasirin yanayi tare da habaka juriya. Sai dai nasarar wadannan yunkurin na bukatar makudan kudade. Alal misali, kasashen Afirka kadai za su bukaci kusan dala biliyan 280 a duk shekara nan da shekarar 2035 don daidaita matsalar sauyin yanayi da rage radadin da suke ciki, adadin da ya zarce karfinsu.
Taron ya cimma yarjejeniyar da kasashen da suka ci gaba za su rika ba da a kalla dalar Amurka biliyan 300 a duk shekara nan da shekara ta 2035, da nufin taimakawa kasashe masu tasowa wajen tunkarar tunbatsar teku da tasirin matsanancin sauyin yanayi. Wadannan kudaden za su je ga kasashe masu tasowa wadanda ke bukatar kudaden don sauyawa zuwa amfani da makamashi da ake iya sabuntawa, da daidaita dumamar yanayi da kuma daidaita barnar da tasirin sauyin yanayi ke haifarwa. Duk da cewa adadin ya ninka dala biliyan 100 a duk shekara na yarjejeniyar da za ta kare a shekara ta 2025, amma bai kai dalar Amurka tiriliyan 1.3 da kasashe masu tasowa ke bukata ba, kuma da yawa sun nuna takaici. (Mohammed Yahaya)