Daraktan cibiyar nazarin kasar Sin dake Nijeriya, Charles Onunaiju, ya bayyana dangantakar Sin da Afrika a matsayin mafi tasiri a duniya, saboda muhimmancinta wajen ba da gudunmuwa ga sauya yanayin nahiyar.Â
Ya ce duk da cewa ana gudanar da dangantakar ne bisa gaskiya da adalci, kafafen yada labaran yamma na neman duk wata kafa ta sukarta da bata mata suna.
Charles Onunaiju, ya bayyana haka ne cikin sharhinsa da jaridar Daily Trust ta Nijeriya ta wallafa.
Ya kara da bayar da misali da wani shirin bidiyo da wata kafar yada labarai ta fitar a baya bayan nan mai taken “Africa-Eye: Racism for Sale” wadda ke nufin amfani da wariyar launi wajen samun kudi, a matsayin wanda ya yi matukar shafawa dangantakar bangarorin biyu bakin fenti. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)