A jiya Talata ne aka bude babban taron tattaunawa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, game da wayewar kai karo na 2 a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin.
A bikin bude taron mai taken “zamanintarwa irin ta kasar Sin da hanyar raya Afirka”, zaunannen wakilin ofishin kungiyar tarayyar Afirka AU a kasar Sin Rahamtalla M. Osman ya bayyana cewa, wayewar kan Afirka da Sinawa, muhimman bangarori ne na tarihin wayewar kan bil Adama a tsawon dubban shekaru.
Ya ce a shekarun baya-bayan nan, yayin da kasashen Sin da Afirka suke mu’amala da koyi da juna ta fuskar wayewar kai, kasashen Afirka suna nuna wa kasashen duniya wayewar kanta mai kayatarwa, da kuma babban tasiri.
Osman ya kara da cewa, kasashen Afirka suna neman samun hanyoyin raya kansu, da zamanantar da kansu, bisa yanayin da suke ciki. Kuma nasarorin da kasar Sin ta samu wajen zamanantar da kanta, sun karfafa gwiwar kasashen Afirka sosai.
A nasa tsokaci yayin taron, wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Afirka, Liu Yuxi, ya ce kasashen Sin da Afirka, suna kokarin samun hanyar bunkasuwa mai dacewa, sun kuma samu gagaruman nasarori a tarihi. Kaza lika abubuwan da suka faru a tarihinsu cikin kusan shekaru 200 da suka wuce, da kuma ayyukansu na samun bunkasuwa, sun sanya Sin da Afirka tsayawa juna a yayin farin ciki da akasinsa, suna kuma gwagwarmaya kafada da kafada da juna, wajen ’yantar da al’ummominsu, kana suna taimakawa juna wajen kiyaye manufar cudanyar sassa daban daban, da kare moriyar bai daya ta kasashe masu tasowa, suna kuma zurfafa hadin gwiwarsu domin samun farfadowa, da samar wa jama’arsu alherai. (Tasallah Yuan)