A yau Lahadi ne aka bude baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin da aka fi sani da “Canton Fair”. Kuma wannan ne karo na 134 da ake gudanar da baje kolin a birnin Guangzhou fadar mulkin lardin Guangdong na kudancin kasar Sin.
Baje kolin zai ci gaba da gudana ne har zuwa ranar 4 ga watan Nuwamba, tuni kuma ya hallara masu baje hajoji, da masu sayen kayayyaki daga sassan duniya daban daban.
- CMG Ya Gudanar Da Taron Bita Yayin Cika Shekara Daya Da Watsa Shirin Leaders Talk
- Wang Yi: Sin Tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Da Adalci Da Lamirin Da Ya Shafi Dan Adam Kan Batun Falasdinu
A cewar kakakin mashirya baje kolin Xu Bing, adadin masu sayayya da suka yi rajistar halartar baje kolin na wannan karo ya haura 100,000, sun kuma zo ne daga kasashe da yankunan duniya sama da 200.
Xu ya kara da cewa, dandalin yanar gizo na baje kolin da aka tanada, zai samar da hidimomi ga masu baje hajoji da kuma masu sayayya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)