Da safiyar yau Asabar 15 ga wata ne, aka kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da fitarwa daga kasar Sin wanda aka fi sani da suna Canton fair karo na 133 a hukumance. Za a gudanar da bikin baje kolin a matakai uku daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, kuma shi ne mafi girma a tarihin baje kolin. Kana fadin wuraren nunin ko kuma adadin masu halartar baje kolin dukkansu sun kai matsayi mafi girma a tarihi.
An bude dakunan baje kolin a hukumance, kuma ‘yan kasuwa da dama na cikin gida da kasashen waje sun yi tururuwa zuwa wajen bikin, wannan shi ne karon farko da aka sake dawo da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da fitarwa daga kasar Sin ido da ido bayan shekaru uku.
Bayanai na cewa, yawan kamfanonin da suke halartar Canton fair na bana ya karu zuwa dubu 34 ko fiye, kana, sabbin kamfanonin da suke halartar bikin ya wuce 9,000, yayin da kamfanoni 39,281 ne suke halartar bikin ta kafar intanet. (Mai fassara: Bilkisu Xin)