Yau Litinin da safe ne, aka bude bikin baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa na kasar Sin karo na 3 a birnin Haikou na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin.
Ana sa ran nuna kayayyakin masarufi masu inganci fiye da 4000 daga kasashe da yankuna guda 65. Yawan kasashe mahalarta bikin da tambura da kuma kamfanoni masu sayayya da sauran ma’aunai sun samu karuwa a bana.
Ban da wannan kuma, kamfanoni da hukumomin sana’o’i daban-daban na lardin Hainan sun bayyana aniyarsu ta shiga bikin, don amfani da wannan zarafi mai kyau wajen yin mu’amala da kamfanonin cikin gida da na waje, tare da kokarin samun moriya tare.
Ciniki ta Intanet wani muhimmin sana’a ce da lardin na Hainan yake goyon baya. Yankin cinikin Intanet tsakanin Sin da ketare ta Sanya, ya halarci bikin a karon farko, tare da gwada amfanin gona da fasaha fiye da nau’o’i 10.
An yi kiyasin cewa, yawan mutane mahalarta bikin zai zarce dubu 300, sassan kasuwanci za su gabatar da ayyukan samar da rangwame iri daban-daban ga masu sayayya a matsayin kiran kasuwa da ma habaka karfin sayayya. (Amina Xu)