Yau Lahadi 5 ga wata ne, aka kaddamar da bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na shida a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin. Bikin na bana, mai taken “more makoma tare a sabon zamani”, wanda ma’aikatar harkokin kasuwanci ta kasar Sin gami da gwamnatin birnin Shanghai suka dauki nauyin gudanarwa, zai kammala ne a ranar 10 ga wata.
CIIE shi ne bikin baje-kolin kasa da kasa na farko na shigowa da kayayyaki a duk fadin duniya. Tun lokacin da kasar Sin ta fara shirya bikin CIIE a shekara ta 2018, kawo yanzu, bikin yana kara samun karbuwa da amincewa daga kasa da kasa. A bana dai, baki daga kasashe da yankuna gami da kungiyoyin kasa da kasa 154 suke halartar bikin, kuma kamfanoni sama da 3400 tare da ‘yan kallo da yawa ne suka yi rajistar halartar bikin. Har wa yau, an tabbatar da halartar wasu manyan shugabannin kamfanonin da suka yi fice a duniya a bikin na bana, wanda ba’a taba ganin irinsa ba a tarihin shirya bikin.
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Yin Iyakar Kokarin Saukaka Rikicin Gaza
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Tattauna Da Masana Tsara Manufofi Da ’Yan Kasuwa Na Amurka
Kasashe 69 gami da wasu kungiyoyin kasa da kasa 3 sun kafa rumfunan baje-kolin kayayyakinsu, ciki har da kasashe 64 da suka halarta cikin kokarin aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya” tare da kasar Sin. Kana, akwai kasashe 11 wadanda a karon farko suka kafa rumfunan baje-koli wajen biki na bana, yayin da wasu kasashe 34 ne da suka baje-kolin kayansu karo na farko a zahirance wato ba ta intanet ba.
Kamar na shekarun baya, ana ci gaba da baje-kolin kayayyakin da suka shafi abinci da amfanin gona, da motoci, da na’urorin fasaha, da kayan masarufi, da na’urorin aikin jinya da kiwon lafiya, da kayan cinikayyar hidimomi da sauransu a bikin na bana. (Murtala Zhang)