A jiya ne aka bude bikin baje kolin fina-finai na kasa da kasa karo na 15 na birnin Beijing, wanda babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG da gwamnatin birnin Beijing suka shirya, a cibiyar taro ta tafkin Yanqi dake birnin Beijing.
Sa’an nan, duk dai a jiya Juma’a, hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin da CMG sun kaddamar da bikin “shekarar habaka kallon fina-finan kasar Sin” a birnin Beijing, domin sanya fina-finai taka karin rawa a kokarin raya bangaren sayayya a kasar. A sa’i daya kuma, CMG ya hada gwiwa da kamfanin da ke kula da babban jirgin ruwan nishadi na Aida Magic City, da kasar Sin ta kera, wajen kaddamar da zirga-zirgar jirgin ruwan mai kunshe da ayyukan kallon fina-finai, duk dai a karkashin wani bangare na bikin “shekarar habaka kallon fina-finan kasar Sin”.
Har ila yau dai a jiya, an gudanar da bikin nuna fina-finai ga jama’a a wani fili karo na 10, wanda CMG da ma’aikatar al’adu ta kasar Cambodia suka hada gwiwa wajen shiryawa, a Angkor Wat na kasar Cambodia. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp