A ranar Alhamis ne aka bude dandalin hadin gwiwa da raya kirkire-kirkire na Sin da Afirka a birnin Wuhan, babban birnin lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin.
Wakilai daga kasar Sin da kasashen Afirka da suka hada da Habasha da Tanzaniya da Afirka ta Kudu suna tattaunawa kan makomar hadin gwiwar kimiyya da fasaha tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Shi ne karo na biyu da ake gudanar da taron a birnin Wuhan.
Ya zuwa yanzu an rattaba hannu kan yarjejeniyoyi 20 kan ayyukan kasa da kasa da suka shafi hadin gwiwar kimiyya da fasaha, wadanda suka kunshi fannonin da suka shafi aikin gona na zamani, da kimiyyar rayuwa da kiwon lafiya zuwa kayayyakin more rayuwa, cinikayyar kasa da kasa da musayar ayyukan jami’o’i.
An kuma ba da sanarwar gasar kirkire-kirkire da kasuwanci tsakanin matasan Sin da Afirka na shekarar 2023 a yayin bikin bude dandalin, don inganta da fadada damar yin kirkire-kirkire da kasuwanci tsakanin matasan Sinawa da ’yan Afirka. (Yahaya Babs)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp