Yau Litinin, an bude dandalin tattaunawar Liangzhu karo na biyu a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang, wanda ma’aikatar al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin, da hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar, da kuma gwamnatin lardin Zhejiang suka dauki nauyi tare.
Dandalin tattaunawa na Liangzhu na wannan karo jigonsa shi ne “mu’ammala da juna da sabon nau’i na wayewar kan bil’adama”, inda aka gayyaci manazarta kan ilmin kayayyakin tarihi, marubuta, da masu kide-kide fiye da 300 daga kasashe da yankuna sama da 60.
Dandalin tattaunawar na mai da hankali kan wasu muhimman fannoni kamar kayayyakin tarihi na al’adu, ilmin adabi da kide-kide, ta gudanar da nazari kan ra’ayoyin musayar wayewar kai mai zurfi, inda aka tattauna hanyoyin da za a bi da kuma hadin gwiwa da za a gudanar, da kuma tattara matsayar da kasashen duniya suka cimma ta aiwatar da shawarwarin wayewar kan duniya. (Safiyah Ma)