Babban birnin Yamai na jamhuriyar Nijar ya karbi a ranar jiya Laraba 26 ga watan Afrilun shekarar 2023, da wani dandalin zuba jari tsakanin Sin da Nijar, shi dai wannan dandali irinsa na farko da birnin Yamai ya karbi bakunci ya gudana a karkashin jagorancin shugaban gwamnatin Nijar, faraminista Ouhoumoudou Mahamadou a cibiyar tarukan kasa da kasa na Mahatma Gandhi da ke birnin Yamai.
Haka kuma wannan na gudana bayan wata ziyarar ’yan kasuwar kasar Sin a ranar Talata 25 ga watan Afrilun shekarar 2023 wanda kuma ta samu ganawa tare da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum duk dai a ranar guda.
A yayin wannan dandalin zuba jari tsakanin kasashen biyu, an samu halartar ’yan kasuwa da masu masana’antun kasar Nijar tare da takwarorinsu na kasar Sin, haka kuma an samu halartar mambobin gwamnatin Nijar da kuma mambobin ofishin jakadancin kasar Sin a Nijar da kungiyoyin ’yan kasuwa da kuma mambobin tawagar ’yan kasuwar kasar Sin CABC. (Mamane Ada)