An bude taron duniya kan fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI ta 2023, jiya Alhamis a birnin Shanghai. Taken taron na bana shi ne, “Hadewar fasahohi: samar da makoma”.
Taron zai gudana ne har zuwa ranar 8 ga wata, kuma ya kunshi muhimman sassa 4 da suka hada da taron karawa juna sani da dandalin tattaunawa, da nune-nune, da gasa, da bayar da lambobin yabo.
Manufar taron na bana ita ce, karin haske kan sabbin hanyoyin da za su kai ga samar da ci gaban masana’antu da fasahohi, da inganta kirkire-kirkire da raya fasahar AI ta zamani na gaba.
Sama da baki 1400 ne suka tabbatar da halartar taron, ciki har da masu lambobin yabo na Nobel da na Turing 4 da sama da malamai 80 daga ciki da wajen kasar Sin, da kuma sama da ‘yan kasuwa 50, daga fitattun kamfanonin fasaha kamar Huawei da Alibaba da Apple da Tesla. (Fa’iza Mustapha)