An bude taron sanin makamar aiki na kasa da kasa mai taken “Cika shekaru 80 da kafuwar MDD: Makomar tsarin duniya, dokokin kasa da kasa, da ra’ayin kasancewar bangarori da dama”, wanda jami’ar Wuhan ta kasar Sin, da jami’ar Benha ta kasar Masar suka hada kai suka karbi bakuncin shirya shi.
Yayin bude taron a yau Asabar a birnin Wuhan na kasar Sin, tsohon mataimakin sakatare-janar na MDD Miguel de Serpa Soares, da babban sakataren kungiyar ba da shawarwari kan shari’a ta Asiya da Afirka ko (AALCO) Dr. Kamalinne Pinitpuvadol, da shugaban jami’ar Benha ta Masar Nasser EL-Gizawy, da farfesa a jami’ar Wuhan Ignacio de la Rasilla, da ma wasu mahalartan taron sun bayyana cewa, dole ne a kare sakamakon nasarar da aka cimma a yakin duniya na biyu, da kuma tsarin duniya da aka kafa bayan yakin yayin da ake tunawa da cika shekaru 80 da kafuwar MDD, da amincewa da gaskiyar tarihi da ta shari’a, wato Taiwan wani yanki ne na kasar Sin, wanda aka tabbatar a wasu takardun dokokin kasa da kasa, ciki har da “Sanarwar Alkahira”, da “Sanarwar Potsdam”, da kuma kuduri mai lamba 2,758 na babban taron MDD, kana da tsayawa kan ainihin ka’idoji na dokokin kasa da kasa, kamar daidaiton mulkin kai, da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida da dai sauransu, da kuma nuna goyon baya ga MDD, don ta taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa, da ma aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori da dama bisa gaskiya. (Bilkisu Xin)