Da safiyar yau Laraba, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) karo na 14, wadda ke zaman majalisar dokokin kasar, ta bude taronta karo na 3, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar sun halarci bikin bude taron, inda firaminista Li Qiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnati ga majalisar dokokin kasar wato majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC domin tattaunawa.
- Dorawa Wasu Laifi Ba Zai Kawo Ci Gaban Da Amurka Ke Muradi Ba
- Kasafin Kuɗin 2025 Taswira Ce Ta ƙarfafa Tattalin Arziki Da Ci Gaban ƙasa – Ministan Yaɗa Labarai
Rahoton ya ce, kasar Sin ta kudiri aniyar samun ci gaban tattalin arzikin da ya kai kusan kashi 5 cikin dari a shekarar 2025. Rahoton ya kuma zayyana jerin wasu muhimman manufofin raya kasa da za a sa gaba a bana, wadanda suka hada da tabbatar da yawan marasa aikin yi na birane da ya kai kusan kashi 5.5 cikin dari, da samar da sabbin ayyukan yi na birane fiye da miliyan 12, da karin kusan kashi 2 cikin dari na farashin kayayyakin masarufi.
Kasar ta samu bunkasar tattalin arziki da kashi 5 cikin dari a shekarar 2024 a karkashin wani muhimmin tsarin manufofi masu tasiri, tare da wasu matakai na habaka samun ci gaba da suka agaza wajen karfafa bunkasar tattalin arzikin. An dai cimma burin manyan manufofi da ayyuka na ci gaban tattalin arziki da zamantakewa cikin nasara a kasar.
Kasar Sin za ta fara bayar da ilimi kyauta ga yara kafin su kai matakin shiga firamare. Wannan kokari da za a aiwatar a mataki-mataki, wani bangare ne na kokarin kasar na gina tsarin ilimi mai matukar inganci.
A cewar rahoton, za a samar tare da aiwatar da wani tsari mai wa’adin shekaru 3, wanda zai mayar da hankali wajen karfafa bangaren ilimi.
Haka kuma, kasar za ta inganta raya ilimin dole mai inganci kuma bisa daidaito, tare da kara bayar da damar shiga makarantun sakandare.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta inganta hada ilimin sana’o’i da ilimi na gama gari, tare da hada hannu da masana’antu da makarantu ta yadda ilimin sana’o’i zai kara dacewa da tsarin ilimi.
Rahoton ya kara da cewa, kasar Sin za ta aiwatar da gyare-gyare a makarantun gaba da sakandare cikin rukunoni, tare da daukar matakai masu kwari wajen fadada ingancin karatu da gaggauta samar da jami’o’i da bangarorin kwarewa da za su kai matsayi mafi kyau a duniya.
Kasar Sin ta ce, tana adawa da duk wani nau’i na kariyar cinikayya da zartar da ra’ayi na kashin kai, kuma za ta daukaka tabbatar da adalci da daidaito a duniya.
Rahoton ya kara da cewa, kasar za ta ci gaba da nacewa ga manufar diplomasiyya mai zaman kanta da bin tafarkin neman ci gaba cikin lumana.
A cewar rahoton, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da sauran kasashen duniya wajen samar da duniya mai adalci da rabuwar iko tsakanin kasa da kasa da dunkule tattalin arzikin duniya, ta yadda kowa zai amfana da ita da inganta aiwatar da shawarar ci gaban duniya da ta samar da tsaro a duniya da ta wayewar kan al’ummun duniya. Haka kuma, za ta shiga a dama da ita wajen aiwatar da gyare-gyare a tsarin tafiyar da harkokin duniya da yayata shawarar gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil Adama da kuma samar da makomar zaman lafiya da ci gaba ga duniya.
Bugu da kari, rahoton ya ce, Sin za ta daukaka burinta na ganin dunkulewar kasar, inda ya ce, za ta inganta cibiyoyi da manufofin raya tattalin arziki da musayar al’adu da hadin kai a fadin mashigin Taiwan da fadada ayyukan raya gabobi 2 na mashigin, ta yadda za a kyautata walwalar daukacin Sinawa na gabobin 2 na mashigin Taiwan na kasar Sin.
Rahoton ya nuna cewa, kasar za ta zurfafa hade dabarun raya masana’antu masu tasowa bisa manyan tsare-tsare da sauran dimbin kokarin karfafa ci gaban wadanda za a kafa nan gaba.
Rahoton aikin ya ce, kasar Sin za ta aiwatar da shirye-shiryen nuna yadda za a yi amfani da manyan sabbin fasahohi, da kayayyaki da tsare-tsaren ciyar da al’amura gaba, da matsa kaimi ga bunkasa harkokin kasuwanci cikin aminci da inganci, da tattalin arzikin kananan jirage masu tashi kasa-kasa, da sauran masana’antu masu tasowa.
Har ila yau, rahoton ya ce, kasar za ta bullo da hanyar da za ta kara samar da kudade ga masana’antun da za a kafa nan gaba da kuma karfafa ci gaban masana’antu kamar na sarrafa halittu, da fasahar daidaita makamashi ta ‘quantum’, da fasahar kere-keren kirkirarriyar basira AI, da kuma fasahar sadarwa ta 6G.
A cewar rahoton, kasar Sin za ta ba da goyon baya ga bunkasa kanana da matsakaitan kamfanoni masu zaman kansu a shekarar 2025, inda ya kara da cewa, kasar za ta ci gaba da zurfafa raya sana’o’in kirkire-kirkire, da inganta ci gaban kanana da matsakaitan masana’antu da ke amfani da fasahohin zamani na musamman domin samar da sabbin kayayyaki da za su kasance daban da na saura.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp