Da safiyar yau Litinin ne aka bude babban taron wakilai na 8, na gamayyar kungiyar masu bukata ta musamman a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran manyan kusoshin gwamnatin kasar sun halarci taron, domin taya murnar bude shi.
A madadin majalissar gudanarwar kasar Sin, mataimakin firaministan kasar Ding Xuexiang, ya gabatar da jawabi mai taken “Aiki tare domin samar da farin ciki, da rayuwa ta gari ga masu bukata ta musamman a turbar zamanantarwa ta kasar Sin”.
Ding Xuexiang ya bayyana farin cikin bude zaman, tare da mika sakon gaisuwa ga rukunin masu bukata ta musamman, da iyalai da abokan su. Ya kuma bayyana matukar godiya ga al’ummar kasar Sin daga fannonin rayuwa daban daban, wadanda ke nuna damuwa, da tallafawa bukatun masu larurar gabobin jiki. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp