Shugaban karamar hukumar Kankara da ke Jihar Katsina ya yi kira al’umma su ci gaba da gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Alhaji Anas ya yi wannan kiran ne a lokacin taro a kan sha’anin tsaro wanda ya gudana a karamar hukumar Kankara.
- Ko Makiyan Buhari Sun San Aikin Da Ya Yi Yafi Na Gwamnatocin Baya -Minista
- Rashin Tsaro Na Kawo Koma Baya Ga Tattalin Arzikin Nijeriya – Buhari
Shugaban karamar hukumar ya ce an tattauna a kan hanyoyin da za a bi don inganta sha’anin tsaro a karamar hukumar.
Ya kara da cewa taron ya kuma fito da wasu dabaru wadanda za a bi domin maganace matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin.
Ya jaddada cewa kokarin da gwamnatin jiha ta yi ya taimaka wajen sake bude hanyar Birji wadda ta tashi daga Kankara zuwa Malali ta isa Zango ta karasa Dansabau bayan an rufe ta shekaru 3 da suka wuce sakamakon ayyukan ‘yan bindiga.
Alhaji Anas ya yaba wa sarakunan gargajiya, jami’an tsaro da mambobin kungiyar sa-kai wajen inganta sha’anin tsaro a yankin.