A yayin da takara a fannin bunkasa Kirkirarriyar Basira wato AI ke ci gaba da karuwa, kwararrun da ke halartar taron dandalin tattaunawa na Beijing na shekarar 2024, sun jaddada bukatar inganta hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da ta Amurka a fannin kirkirarriyar basira ta AI.
Graham Webster, masani a jami’ar Stanford ya bayyana a yayin taron cewa, Sin da Amurka na daga cikin manyan kasashen da ke kan gaba a fannin kirkirarriyar basira ta AI, tare da samun manyan dakunan gwaje-gwajen AI, da manyan samfuran kwamfutoci masu sarrafa bayanai da suka zarce takwarorinsu na duniya.
- Shugabannin Kasashen Waje Za Su Halarci CIIE Karo Na 7
- Dalilin Da Yasa Kaduna Ke Kan Gaba A Samar Da Kuɗaɗen Shiga A Arewa – Shugaban KADIRS
Webster ya ce, gaba daya raba-gari tsakanin bangarorin biyu zai haifar da mummunan sakamako.
Haka ma, Karman Lucero mai bincike na cibiyar kasar Sin ta Paul Tsai dake jami’ar Yale, ya jaddada muhimman darussa da za a iya koya daga kwarewar kasar Sin, saboda kasar Sin tana da muhallin tafiyar da harkokin AI mai cike da kuzari kuma mai fadi.
Lucero ya ce, yanayin da ya fi dacewa don samar da fahimtar juna da kuma kaucewa matsaloli a tsakanin bangarorin biyu ya ta’allaka ne kan tattaunawa, ba wai tattaunawa ta gwamnati kadai ba, har ma da bin hanyar tattaunawa da mu’amala tsakanin jama’a. (Yahaya)