Gidauniyar Zakka da Wakafi mai zaman Kanta a Jihar Kaduna ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Uba Sani, da ta samar da wata hukuma da za ta rika kula da harkokin Zakka da Wakafi a jihar, wanda hakan zai taimaka wajen ragewa al’umma radadin talauci.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin daya daga cikin mamba a gidauniyar, Malam Abdullahi Babayaro, a zantawarsa da manema labarai. Ya ce, idan gwamnati ta samar da wata hukuma ko cibiya mai kula da lamuran Zakka, babu shakka zai taimaka mata wajen samun damar tallafa wa al’umma marasa karfi. Ya ce, ita Zakka tana rage wa al’umma radadin talauci ne.
Malam Babayaro, ya ce rashin fitar da zakka illa ce babba wajen ci gaba al’umma baki daya, inda ya yi kira ga masu hannu da shuni da su fitar da dukiyarsu wajen tallafa wa rayuwar al’umma kamar yadda addnin Islama ya tanada.