Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta fara aikin samar da wutar lantarkin ta madatsar ruwan (Mambila Hydro Power Project) a jihar Taraba, domin samun ci gaba a yankin baki daya.
Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a bukin cika shekaru 10, na Mai Martaba Sarkin Mambila, Dakta Shehu Baju II, a karamar hukumar Sardauna ta jihar Taraba.
- Samar Da Tsaro: Ribadu Ya Yaba Wa Sarakunan Gargajiya A Adamawa
- Za Mu Garzaya Kotun Koli Don Daukaka Kara Kan Zaben Gwamnan Adamawa- APC
Gwamnan wanda shi ne shugaban taron, da ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Awwal Bamanga Tukur, ya jaddada mahimmancin irin wadannan ayyukan samar da wutar da cewa zai taimaka ga ababen more rayuwa da bunkasa tattalin arziki, da ma inganta rayuwar jama’a.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi kira ga al’ummar yankin Mambila da su rungumi zaman lafiya da hadin kai, tare da sanin muhimmancin zaman lafiya wajen samar da ci gaba a tsakanin al’umma.
Gwamna Fintiri ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa da kokarin samar da ci gaba a tsakanin jihohin Adamawa da Taraba, ya kuma bayyana bukatar samar da ayyukan more rayuwa don bunkasa ci gaban yankin.
A jawabinsa na fatan alheri a taron Sarkin Wukari, Aku Uka, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiyar jihar Taraba, Manu Ishaku, Ada Ali, ya bukaci mai masaukin biki da sarakunan gargajiya a jihar da su goyawa gwamnatin jihar baya wajen ganin an samar da zaman lafiya a jihar ya kuma yaba da goyon bayan da jama’ar masarautar ke baiwa masarautun gargajiya ta Mambila.
Da yake jawabin godiyar mai masaukin biki, Dakta Shehu Baju II, ya bayyana godiya da jin dadinsa ga duk wadanda suka bayar da gudumawa na ganin taron ya samu nasara, ya kuma yi godiya ta musamman ga hakimai da manyan baki, jama’a da masu hannu da shuni bisa goyon bayan da suka bayar.