Jami’an tsaron Umrah a Saudiyya sun kama wani mutum da aka bayyana cewa dan kasar Yemen ne, tare da mika shi ga mahukunta don fuskantar shari’a bisa laifin buga daga Bana a Harami.
Babban Jami’in Tsaro a kasar ne ya bayyana kama mutane da suka saba wa ka’idojin Umrah da kuma keta alfarmar Masallacin Harami.
Saudiyya Ta Kama Mutumin Da Ya Yi Umrah Saboda Sarauniyar Ingila
Tun da farko wani faifan bidiyo ya bazu a shafukan sada zumunta wanda ya nuna wani mutum a Ihrami yana daga tuta/bana da ke bayyana mutumin a matsayin wanda yake aikin Umrah a madadin marigayiya Sarauniyar Ingila.
Shugaban kula da harkokin masallatan Harami guda biyu ya fitar da sanarwa inda ya bukaci maziyarta cewa, Masallatan Harami guda biyu wuraren ibada ne na Allah shi kadai, ba wai don wani ba ko daga tutoci da bana ko fastoci da suka saba wa ka’ida da umarni ba.