Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewar ta bayar da goyon baya ga farmakin da jami’an tsaro suka ceto sama da mutane 250 da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a cikin shekara daya da ta gabata.
Mashawarci na Musamman ga Gwamnan Sakkwato kan sha’anin tsaro, Ahmad Abdul Usman ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a yau tare da cewar tuni wadanda aka ceto suka koma cikin iyalansu.
- MDD Ta Amince Da Kudirin Sin Na Kafa Ranar Tattaunawa Tsakanin Wayewar Kai Na Duniya
- Kotu Ta Yanke Wa Matar Alkali Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya A Kebbi
Ya ce sun samu wannan nasarar ne a bisa ga ingantaccen hadin kan da ke akwai tsakanin gwamnatin jiha ta hannun Sashen Kula da Sha’anin Tsaro da Jami’an Tsaro tare da cikakken goyon bayan Rundunar Sojin Sama a wuraren da ake fama da kalubalen tsaro.
Haka ma ya ce a cikin shekara daya Gwamnatin jiha ta kaddamar da Rundunar Tsaro ta jiha domin marawa jami’an tsaro baya wajen yakar matsalolin tsaro a Kananan Hukumomi 13 da lamarin ya fi ta’azzara.
Ya ce domin samar da ingantaccen yanayin aiki, gwamnatin jiha ta bayar da motoci 40 ga sabuwar Rundunar Tsaro ta jiha., haka ma a yanzu haka an kammala shirin ba su babura 1, 000 domin gudanar da aiki yadda ya kamata.
Mashwarcin na Gwamna ya kuma ce sun biya bashin alawus da jami’an tsaro ke bin gwamnatin bashi tare da kara yawan kudaden domin kara karfafa masu guiwar aikin da suke yi ba dare ba rana wajen kawar da ayyukan ta’addanci da wanzar da zaman lafiya a Jihar.