A ranar 5 ga watan Satumba da karfe 1 saura mintuna 8 ne, girgizar kasa mai karfin maki 6.8 ta afku a gundumar Luding dake yankin Ganzi na lardin Sichuan.
Bayan aukuwar bala’in, gwamnatin tsakiya da ta wurin, sun kaddamar da aikin ceto nan da nan. Ya zuwa yanzu, an tura masu aikin ceto fiye da dubu 13, ciki hadda sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin da rundunar ‘yan sanda masu dauke da makamai da rukunin ‘yan kwana-kwana da soji na musamman da jiragen saman aikin ceto da rukunonin aikin ceto dake kula da yanayin ko ta kwana da kungiyar aikin jiyya da sauransu.
Yawan mutanen da suka kubutar ya kai 650, yayin da aka tsugunar da mutane fiye da dubu 60 da iftila’i ya ritsa da su.
Ban da wannan kuma, ya zuwa karfe 5 da yammacin jiya, yawan kudaden tallafi da lardin ya samu ya kai kusan RMB Yuan biliyan 1.2. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp