Mahukuntan kula da gasar Premier League sun ci tarar kungiyar kwallon kafa ta Fulham £75,000, an kuma dakatar da ita wata shida daga daukar matasan ‘yan wasa a duniya.
Kenan ba dama ta yi rijistar matasan ‘yan wasanta da suke makarantar horon kungiyar ko kuma dauko wasu daga wasu wuraren, sannan hukuncin ya kunshi wani biyan kudi da kungiyar ta yi wa Balham Blazers FC da ta kai dan wasa Fabio Carbalho ya koma Liverpool.
- Sauya Sheka: Jam’iyyu Na Shirin Tilasta Kafa Dokoki Masu Zafi A Kan ‘Yan Majalisa
- Arsenal Ta Sake Tabbatar Da Cancantar Lashe Firimiya
Cavalho, dan wasan gaba mai zura kwallo a raga ya koma Fulham daga Balham Blaz-ers a Disambar 2014, sannan Premier League ta ce Fulham ta amince da cewar ta kar-ya dokar da ta shafi daukar matasa ta hukumar.
An jingine hukuncin daga shekara daya, kenan ya fara aiki daga 15 ga watan Afirilun 2024, sai dai Fulham tana ta 12 a kan teburin Premier League, bayan cin wasa 12 da canjaras bakwai aka doke ta wasa 16 sannan ta zura kwallo 51 a bana an zura mata 55 a babbar gasar firimiya ta Ingila.