Babban sakataren hukumar kula da asibitocin Jihar Kano, Dakta Mansur Nagoda, ya amince da dakatar da wani jami’in lafiya a asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase.
Dakatarwar na zuwa ne sakamakon korafe-korafe da yawa da aka samu daga majinyata da ma’aikata game da rashin zuwa aikin likitan ba tare da sanarwa ba.
- An Kashe Kasurgumin Dan Bindiga Modi Da Yaransa 4 A Katsina
- Hukumar NSCDC Ta Kama Wasu Mutane 9 Da Ake Zargi Da Aikata Fashi A Kano
A cewar Dokta Nagoda, likitan da aka dakatar “wanda aka sakaya sunansa”, ya bar wajen ba tare da sanar da hukumar asibitin ba.
Ya bayyana cewa an yi ta kiraye-kirayen da yawa ga likitan da aka dakatar, amma ta ci gaba da amsawa tana cikin harabar ba tare da ta kasance a cikin dakin likitocin ba kuma ba ta fito ba har sai da safe, wanda hakan ya sa mai ciwon siga a cikin ruɗani.
Sakataren zartarwar ya kara da cewa ya kamata a ce rantsuwar da likitocin suka yi na kare rayuka da dukiyoyin su zama farkon abin da za su fara yin aiki a cikin tsarin sannan ya bukaci kowa ya tashi tsaye.
“Bari wannan ya zama gargadi ga kowa, idan ta kowace hanya dole ne ka kasa aiki, yana da matukar muhimmanci ka yi tsari mai kyau da wani likita domin ya rufa maka aiki, ba za mu nade hannayenmu muna kallon yadda kowa yake abin da yake so ba.”
Nagoda ya kara da cewa dakatarwar za ta ci gaba da aiki har sai an kammala bincike, tare da jaddada kudirin hukumar na tabbatar da rikon amana da kwarewa a tsakanin ma’aikatan kiwon lafiya.
Nagoda ya yi gargadin cewa “Hukumar zartaswa za ta ci gaba da aiki da karfi kuma muna sa ran duk wanda sunansa ya bayyana a cikin jerin sunayen aiki zai kasance a bakin aiki, kana idan mutum ya samu wata matsala ya kuka da kansa.”