Wata kotun yanki da ke garin Jos ta Jihar Filato, ta daure wani bakanike mai suna James Mathew wata 3 a gidan gyaran hali bisa laifin satar batirin mota.
Alkalai biyu da suka jagoranci shari’a, Ghazali Adam da Hyacinth Dolnaan, suka yanke masa hukuncin bayan ya amsa laifinsa.
- Chelsea Tana Tattaunawa da Manchester City Kan Sayalen Sterling
- Kwankwaso Ba Zai Yi Wa Peter Obi Takarar Mataimaki Ba — NNPP
Sai da alkalan sun ba shi zabin biyan tarar N10,000.
Tun da farko mai gabatar da karar Insfecta Monday Dabit, ya bayyana wa kotun cewa a ranar 21 ga watan Mayu wani mai suna Daflok Maknop ya shigar da kara a ofishin ‘yan sanda na ‘A’, Division’ na garin Jos.
Mai gabatar da karar ya ce, wanda aka yanke wa hukuncin, ya balla motar Maknop, inda ya sace batirin motar da aka kiyasta kudinta ya kai N15,000.
Ya kuma ce, laifin ya saba wa sashe na 272 na kudin dokar fanel kot.