Kotun musulinci da ke zamanta a unguwar Danbare ta daure wani Maiunguwa bisa zargin sace janareta da kofofi a wani kangon, an daure wannan mai unguwa ne bayan da aka tuhume shi da aikata laifuka da suka hada da shiga wurin ba da izni ba da kuma sata.
Tun da fari, dansanda mai gabatar da kara Sufeto Bashir, ya shaida wa kotu cewa, rundunar ‘yansanda ta kamo mai unguwar ne bayan wani bakanike ya kai musu rahoton sace masa janareta da wasu kayayyaki a kangon da yake ajiye kayan aikinsa., daga nan ne kuma bincike ya kai ga kamo mai unguwar kuma suka gurfanar da shi gaban kotu. To sai dai mai unguwar ya karyata zargin.
Alkalin kotun mai shari’a Munzali Idris Gwadabe, ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan Yari, sannan ya daga shari’ar zuwa 18 ga oktoba.