Hukumar kula da bayanai ta kasar Sin, ta ce an fara rajista a dandalin samar da bayanai na kasar a jiya Asabar.
An bude dandalin wanda za a iya shiga ta adireshin website https://sjdj.nda.gov.cn domin yin rajista, lamarin da ya zama muhimmin matakin ci gaba a fannin gyare-gyaren da suka shafi sakarwa kasuwanni mara ta fuskar samun bayanai.
- Kamfanoni 10 Sun Zuba Jarin $466m A Jihar Nasarawa
- An Samu Karuwar Jigilar Kayayyaki A Sabuwar Tashar Jigila Da Ta Hada Sin Da Kasashen Ketare
A ranar farko ta rajistar, dandalin ya gabatar da rukunonin bayanai, ciki har da na inshorar lafiya da yanayi da albarkatun kasa.
Jigon shirye-shiryen da suka shafi bayanai na kasar Sin a bana shi ne, inganta rawar da bayanai ke takawa wajen rage tsadar tafiyar da harkokin kamfanoni da inganta sabon karfin samar da hajoji da hidimomi da ingiza ci gaba mai inganci.
An yi kiyasin cinikin da aka yi a kasuwar bayanai ta Sin ya zarce yuan biliyan 160 kwatankwacin dala biliyan 22.3 a shekarar 2024, inda aka samu karuwar sama da kaso 30. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp