A ranar 28 ga watan Fabarairun da ya shude ne aka saki wani fim din kasar Sin mai lakabin “Creation of the Gods II: Demon Force”, a gidajen kallon sinima 39 dake sassan tarayyar Najeriya, da kuma wasu 2 dake kasar Ghana, da sinima 1 a Laberiya.
Wannan ne dai karon farko da aka saki wani fim da aka shirya a kasar Sin kai tsaye, a allunan sinima na kasashen yammacin Afirka. Kuma a cewar wani manajan gidan sinima dake Abuja, fadar mulkin Najeriya, duk da kasancewar fim din shi ne na farko da ya shiga gidajen kallon na kasuwanci a birnin, jigon labarin ya samu karbuwa matuka tsakanin masu kallo. Ya ce shigar fina-finan Sin kasuwar gidajen kallo a kasar zai kara karsashin kasuwar fina-finan kasar.
Ana sa ran ci gaba da haska wannan fim har zuwa ranar 6 ga watan nan na Maris. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp