A yau Asabar ne kasashen Sin da Amurka suka fara wani babban taron tattalin arziki da cinikayya na matakin koli a birnin Geneva na kasar Switzerland.
A matsayin shugaban tawagar kasar Sin kan harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Amurka da Sin, He Lifeng, wanda mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan kasar, ya halarci taron tare da jagoran tawagar Amurka, babban sakataren baitul-malin kasar, Scott Bessent. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp