Kungiyar masana’antu da kasuwanci ta Sin ta fitar da jerin manyan kamfanoni masu zaman kansu na Sin guda 500 na shekarar 2023. Kamfanonin JD, da Alibaba (Sin), da Hengli su ne manyan kamfanoni uku dake kan gaba a jerin.
Babban sakataren kungiyar masana’antu da kasuwanci ta Sin, Zhao Dejiang, ya bayyana cewa, yawan jarin da kamfanonin dake cikin jerin suke mallaka ya kai yuan a kalla biliyan 27.578, wanda ya karu da yuan biliyan 1.211 bisa shekarar bara. Sannan yawan jarin da kamfononin kera kayayyaki suke mallaka a cikin jerin ya kai yuan a kalla biliyan 14.516, wanda ya karu da biliyan 1.944 bisa na shekarar bara. Kana yawan jarin da kamfanonin ba da hidima suke mallaka a cikin jerin ya kai yuan a kalla biliyan 31.404, wanda ya karu da biliyan 1.289 bisa na shekarar bara.
Kamfanonin dake cikin jerin suna dora muhimmanci kan kirkire-kirkire na fasahohi, kuma a ciki akwai kamfanoni guda 414 da suka sami muhimman fasahohi ta hanyar nazari, da samarwa da kansu. Kuma kamfanoni 432 ne suka mayar da sakamakon kimiyya da fasaha da suka samu ta hanyar tattara jari da kansu.
Ban da wannan, a cikin kamfanonin dake cikin jerin, fiye da 90% za su tsara shiri, ko sun riga sun tsara shirin mayar da kansu zuwa kamfanoni na zamani a fannoni daban daban. Kana kusan kaso 90% na kamfanonin dake cikin jerin sun dauki matakai iri iri na gudanar da ci gaba maras gurbata muhalli ta hanyoyi iri iri. (Safiyah Ma)