An fitar da rahoto mai taken “Kasar Amurka ta keta hakkin dan Adam na makaurata da ‘yan gudun hijira” yau Alhamis 30 ga wannan wata, inda aka nuna laifuffukan da Amurka ta aikata kan batun game da makaurata da ‘yan gudun hijira ta hanyar amfani da abubuwan da suka faru da alkaluman da aka samu, rahoton da ya shaida cewa, Amurka ba kasa mai ba da misalin demokradiyya da ta saba kiran kanta ba ce, a maimakon haka, tana baza karairayi, kuma tana nuna fuska biyu a ko da yaushe.
Rahoton ya yi nuni da cewa, Amurka tana daukar matakan keta hakkin dan Adam na makaurata da ‘yan gudun hijira iri daban daban, har ta kafa tsarin tsare makaurata mafi girma a duniya. Dalilin haka shi ne manufar wariyar launin fata da take aiwatarwa.
A karshe rahoton ya jaddada cewa, gwamnatin Amurka ta nuna bambanci ga kusan daukacin mutanen da suka kaura zuwa kasar daga sassan duniya. Ban da haka gwamnatin Amurka tana tsoma baki a cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya, tare kuma da tayar da yake-yake, da haifar da masifun jin kai da rikicin ‘yan gudun hijira, har ta dorawa sauran kasashen duniya laifuffukan. (Mai fassarawa: Jamila)